Kafa giidauniyar masu fama da yunwa a Afrika

Image caption Kasashen kusurwar Afrika na fama da karancin abinci

A yayin da wasu kungiyoyin agaji a Birtaniya sun kaddamar da wata gidauniyar tara kudi don agaza ma mutane fiye da milyan goma da mummunan fari ya shafa a kusuwar gabacin Afrika an samu munanan labarari na illar farin a kan jama'a.

Kungiyoyin agaji a sansasanin yan gudun hijira na Dadaab sun sheda wa BBC cewa a shirye wasu matan suke su bar 'ya'yansu da suka rani su mutu, idan har za su iya tsirar da sauran yaran nasu daga fama da yunwa. Kamar mutane dubu biyar ne a kowace rana suke tafiya a kasa daga Somaliya don isa sansanonin da ke Ethiopia da Kenya.

A karon farko an faa samun cikakkun bayanai game da girman yadda matsalar fari ke shafar mutanen dake tserewa daga kasaar Somalia zuwa Habasha, a yankin kusurwar gabashin Afrika.

Hukumar samar da agajin abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane sama da dubu dari da goma sun isa wasu sansanoni dake Dolo Ado, a sashen Kudu maso gabashin Habasha.

Sansanonin yan gudun hijira na Dolo Ado, tuni suka cika suka batse, yayinda wasu mutanen kimanin dubu da dari shidda ke ci gaba da kwarara ko wacce rana.

Sun galabaita sakamakon tsananin yunwa, ga kuma gajiyar tafiyar da suka yi ta kwana da kwanaki tare da yara kanananda ke fama da karancin abinci, inda suka hauro da su daga Somalia.