Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi ki yaye: Shayarwa tsakanin ma'aikata

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Shirin na wannan makon zai maida hankali ne kan shayar da nonon uwa a tsakanin mata ma'aikata ko 'yan kasuwa 'yan boko da dai sauransu.

Wani bincike da aka gudanar a Birtaniya a bara kan yadda ake shayar da yara ya nuna cewa an samu karuwar matan dake shayar da 'ya'yansu nono zuwa kashi 81 cikin dari a fadin kasar.

Binciken wanda ake gudanarwa duk bayan shekaru hudu ya nuna cewa karin kashi 81 cikin dari da aka samu ya kunshi karin kashi biyar cikin dari daga sherarar 2005 zuwa shekarar 2010 da kuma karin kashi kashi goma sha biyu cikin dari da aka samu tun shekarar 2000.

Nasarar dai an alakanta ta ne da irin wayar da kan da ake na cewa nono uwa shine abinci mafi inganci ga jarirai.

Domin bayanai daga hukumar lafiya Birtaniya NHS sun nuna cewa a cikin yara goma da aka haifa ana shayar da takwas daga cikinsu akalla sau daya bayan an haife su. wanda a ada a shekarun 1990 ake samun shida cikin goma.

Sai dai kuma al'kaluman ba su nuna yawan iyaye matan dake shayar da nono zalla ba har zuwa tsawon watanni shidan da ake bada shawara.

A cewar hukumar lafiyar ta Burtaniya NHS komawa bakin aiki ko karatu ba ya na nufin mace za ta daina shayar da nono zalla ba, domin ya na da kyau ta shirya yadda za ta yi gabannin komawarta aiki ta yadda za ta ginda samun damar shayar da jaririnta kamar yadda yakamata.

Hukumar ta bada wasu shawarwari da suka hada da neman wajen renon yara dake kusa da gurin aikinta, inda za ta iya amafani da lokacin cin abincinta wajen zuwa ta baiwa jariri nono.

Haka kuma yana da kyau mace ta shayar da jaririn sosai da yamma bayan ta tashi daga aiki ko makaranta ko kuma dai duk inda taje da ya hana ta samun damar da shi sosai a ranar.

Haka kuma hukumar ta bada shawarar cewa iyaye mata za su iya amfani da dabarar na ta tatsan ruwan nono su bari domin a baiwa jariri a duk lokacin da ya bukata kafin su dawo gida.

To yayinda Birtaniyar ke ganin ta samu nasarar samun karuwar mata masu shayar da nono, kuma ta ke kara karfafa musu guiwa wajen bada nono zalla har tsawon watanni shida, a wasu kasashen nahiyar Afrika da suka hada da Nijar da Najeriya wasu mata ma'aikata na daina yin cikakkiyar shayawar da ta kamata da zarar sun koma bakin aiki.

A yi sauraro lafiya.