Hukuncin kisa kan wata 'yar fim din Hausa

Hukuncin kisa kan wata 'yar fim din Hausa
Image caption A yanzu hankali zai karkata ne kan mahukunta a jihar Kano

Kotun kolin Najeriya ta tabbatar da hukuncin kisan da kotun daukaka kara ta yanke wa wata 'yar fiim din Hausa Rabi Isam'il bayan da ta nutsar da saurayinta a ruwa a shekara ta 2002.

Kotun tarayya ce da ke Kano ta yanke mata hukuncin kisa ta hanyar ratayewa, bayan da same ta da laifin kashe saurayinta Auwalu Ibrahim.

Masu gabatar da kara sun ce ta baiwa saurayin nata guba ne sannan ta nutsar da shi a wurin shakatawa na Tuga a jihar Kano a watan Disamban 2002.

Masu shigar da kara sun zargi Rabi Isam'il da kashe saurayin nata domin ta kwashe dukiyarsa.

Sai dai rabi ta daukaka kara zuwa kotun koli - kuma a yanzu kotun ta tabbatar da hukuncin kotun kolin.

Da take mayar da martani ga hukuncin, lauyar gwamnatin jihar Kano wacce ta shigar da karar, Binta Lawal ta ce gwamantin ba wai tana murna bane da hukuncin kisan da aka yankewa matarba, illa dai kawai suna son tabbatar da adalci ne ga duka bangarorin biyu.

Lauyoyin wacce ake karar dai ba su uffan ba kan hukuncin kotun kolin.

A yanzu dai hankali zai koma kan mahukunta ne a jihar ta Kano, domin ganin yadda za su tunkari hukuncin na kotun kolin.