Za a Binciki jaridar News of The World

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Pira Ministan Burtaniya, David Cameron

Fira Ministan Burtaniya, David Cameron, ya bayyana cewa ya kafa wani kwamiti da alkali zai jagoranta domin binciken zargin nadar bayanai ta waya da ake yiwa wata jaridar kasar wato News of the World.

Mista Cameron ya ce duk da cewa dai 'yan sanda na binciken lamarin, kamata ya yi a kara nazari akan al'amarin domin duba dokokin tafiyar da harkar jarida a kasar.

Fira Ministan ya ce wannan ne yasa za'a kafa wani kwamiti mai zaman kasa da alkali zai jagoranta domin duba al'amarin.

Har wa yau Mista Cameron ya bayyana kusancin 'yan siyasa da kuma 'yan jarida a matsayin wani abu dai bai kamata ba, inda ya ce batun nadar bayanai ya bullo da wani babi a kasar.

Shi dai Kamfanin News International ya yi shelar rufe jaridar News of the World, sakamakon cece- kucen da badakalar satar bayanan wayar salula ta janyo.

A ranar Lahadi mai zuwa ne dai za a buga jaridar ta karshe.

Shugaban kamfanin News International James Murdoch ya amince da cewa jaridar ta gaza gano musabbabin abin da ya kira kuran- kuran da ta rika maimaitawa .

Jaridar The Guardian wacce ita ce fasa-kwai dangane da satar bayanan wayoyin salula ta ce tsohon editan jaridar News of the World Andy Coulson, wanda daga baya ya yi aiki a matsayin mai baiwa Fira Ministan Burtaniya David Cameron shawara kan harkokin sadarwa, za a kama shi idan an jima a yau bisa tuhumar da ake masa akan cewa yana da masaniya dangane da batun satar bayanan wayoyin salula.

Ko da yake Mr Coulson ya sha musanta wannan zargin.

A yau ne dai gwamnatin kasar za ta kammala tattaunawar neman shawara akan matakin da za a dauka, sai dai idan an yi la'akari da dubban sakonnin mutane da za a karanta akwai yiwuwar cewa matakin zai dauki lokaci.