Sojoji biyar za su gurfana gaban kotu a Maiduguri

Wasu mazauna Maiduguri suna shirin yin kaura
Image caption Wasu mazauna Maiduguri suna shirin yin kaura

Rahotanni daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno da ke arewacin Najeriya, sun ce Babban Hafsan Hafsoshin Sojin kasar, Air Marshal Oluseyin Petinrin, ya ce za a gurfanar da wadansu sojojin Rundunar JTF da ke Maidugurin su biyar a gaban sharia, bisa zargin wuce gona da iri a ayyukansu.

Rahotannin sun ce ya furta hakan ne, sakamakon zargin da jamaa ke yi cewa sojoji na karkashe jamaar da ba su ji ba su gani ba ayakin da suke yi da 'yan kungiyar Boko Haram.

Kakakin Rundunar ta JTF, Kanar Hassan Ifeji Muhammad, ya shaidawa BBC cewa duk wani sojan da ya yi laifi wajibi ne a gurfanar da shi a gaban shari'a.

Kanar Muhammad ya ce laifuffukan da za su iya tilasta gurfanar da sojoji a gaban shari'a suna da yawa: "mutum ya kashe mutum kuma ba a ce ya kashe shi ba; na biyu, ka je sata; (laifuffukan) da yawa".

Sai dai bai bayani a kan irin laifuffukan da ake tuhumar sojojin biyar da aikatawa ba; a cewarsa, "ban sani ba ko wanne laifi suka aikata-wannan ba zan fada maka ba saboda ban sani ba".

Kungiyoyin kare hakkin bil-Adama na gida da na waje dai sun zargi sojojin da kashewa da kuma cin zarafin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, zargin da rundunar sojin kasar ta sha musantawa.