Syria ta zargi Amurka da rura rikici

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jakadan Amurka a Syria, Robert Ford

Wata mai baiwa shugaban kasar Syria shawara, Buthaina Shabaan, ta zargi jakadan Amurka da rura wutar rikici a kasar wajen taimakawa masu zanga-zangar kin jinin gwamnati.

Ms Shabaan ta ce jakadan Amurka Rober Ford ya kai wata ziyara da ba'a amince ba a birnin Hama inda kuma ya tattauna da malaman addini da kuma kungiyoyin fararen hula abun da kuma ta ce ya keta doka.

A ranar lahadi ne dai za'a a fara taron sulhu a kasar.

Mai baiwa shugaban kasar shawara ta zargi jakadan da mu'amala da kungiyoyi masu daukar makamai, wanda kuma ke tada zaune tsaye a birnin Hama.

'Yan adawa a kasar sun ce sama da masu zanga-zangar duba daya da dari uku ne suka mutu, tun da aka fara zanga-zangar kin jinin gwamnati a kasar.