Za'a maida tsohon shugaban Chadi gida

Za'a maida tsohon shugaban Chadi, Hissene Habre zuwa kasarsa ta haihuwa daga Senegal bayan ya shafe fiye da shekaru ashirin yana gudun hijira.

Dama dai kasar ta Chadi da wasu kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun sha kiraye kirayen a mai da shi gida don ya fuskanci tuhumar da akeyi masa ta kisan dubban mutane a lokacin mulkin sa.

Senegal din dai bata bada dalilin maida shi gida ba, amma tace a jibi litinin ne, insha Allahu wani jirgi zai tashi ashi zuwa chadi.