Hauhawar farashin kaya a Sin na yiwa Hukumomi barazana

Hakkin mallakar hoto Reuters

Adadin hauhawar farashin kayan masarufi a Kasar Sin wato China ya yi saman da bai ta ba yi ba cikin shekaru uku.

Wannan dai ya faru ne duk da irin rage- ragen da aka yi ta yi a kudin ruwan kasar da kuma rage bashin banki.

Adadin farashin kaya a watan Yunin da ya gabata ya karu da fiye da Kashi Bakwai cikin Dari, akan yanda ya ke a Watan Mayu.

Rahotanni dai na bayyana cewa Hukumomin Kasar Sin sun nuna matukar damuwar su akan hauhawar farashin kayan abinci da na man fetur wanda ka iya janyo rashin kwanciyar hankali a Kasar.

Farashin naman Alade, wanda ya na daya daga cikin mahimman abincin 'yan Sin ya yi sama sosai, ya yin da kuma ambaliyard ruwa ta yi wa Yankin matukar illa.