An samu fashewar bam a daren Jiya a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto AFP

A Maiduguri babban birnin Jihar Borno, a daren jiya ne aka samu fashewar wani abu da ake kyautata zaton bom ne, a wasu unguwanni dake kusa da London Ciki.

Mazauna tsakiyar birnin Maiduguri da dama sun bayyana jin karar tashin bom din, in da da ga bisani su ka ce sun rika jin karar harbe- harben bindigogi.

A unguwanni kamar su Dikwa Lowcost kuwa wasu Jama'a sun ce tun kimanin sa'o'i uku kafin tashin bom din su ka fara ganin wasu takardu masu dauke da gargadin cewar Jama'ar dake wurin su kaurace.

Tun daga daren Jiya kawo ya zuwa safiyar Yau ba a ji wasu bayanai daga Hukumomin ba game da abkuwar lamarin.

Sai dai wasu majiyoyi sun bayyana cewa sun ga Jami'an Soji biyu da suka jikkata a lokacin da ake garzayawa dasu asibiti.