An kaddamar da sabuwar Kungiyar kare dan adam a Nijar

Hakkin mallakar hoto AFP

A Jamhuriyar Nijar an yi bikin kaddamar da wata sabuwar Kungiyar farar hula a birnin Yamai.

An yi wannan bikin ne a jiya inda aka kaddamar da Kungiyar wadda ke kula da kare hakin dan adam.

Babban gurin da wanann kungiya ta sa a gaba shi ne aiwatar da duk wasu ayyukan kyautata jin dadin rayuwar Jama'a da suka hada da bunkasa tattalin arziki, da ilmi, da kiwon lafiya, da samar da ruwan sha tsabtacce da dai sauransu.

Domin tafiyar da ayyukan na ta, Kungiyar ta ce a shirye ta ke ta hada gwiwa da duk wata Kungiya ta ciki da wajen Kasar ta Nijar, muddin dai manufofin su sun zo daya.

A ranar 1 ga wannan watan na Yuli ne Gwamnati ta fitar da takardar bai wa Kungiyar izinin gudanar da ayyukanta.