Neman agaji ga jama'a a Somalia

Shugaban hukumar kula da masu gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Anthonio Gutterres yace yana son kungiyoyin agaji na kasa da kasa su taimaka wa Somalia don shawo kan bala'in farin dake addabar kasar.

A wata Hira da BBC Mr Gutterras yace yayi imanin cewa majalisar Dinkin Duniya na magana da hukumomin Somalia don ganin yadda za'a shawo kan matsalolin tsaro saboda a iya kai kayan agaji.

Ya kuma ce farin da ake fama dashi a Somalia yafi na ko ina a yankin, kuma jama'a dadama na makale a kasar, sun kasa isa sansanonin 'yan gudun hijira a Kenya da Habasha