Shugaba Al Bashir ya nemi da a janyewa Sudan takunkumi

Hakkin mallakar hoto Reuters

Shugaban Kasar Sudan Omar Al-Bashir, ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da Amurka kan su cire wa Kasar sa takunkumin da aka aza mata, sakamakon rikicin da ya dabaibaye Kasar tsawon Shekaru da dama.

Shugaba Al-Bashir ya gabatar da wannan bukata ne a lokacin bikin taya Sabuwar Kasar Sudan ta Kudu samun 'yancin kai.

A bangare guda kuma Yankin Darfur wanda ke cikin yankunan da aka dade ana tafka rikici a Sudan, ya yi silar samar da 'yan gudun hijira da dama, wadanda suka bar gidajensu dalilin dauki- ba- dadi tsakanin 'yan tawaye da Sojojin Gwamnati.

Mutanen yankin na Darfur dai na korafin cewa Gwamnatin Khartoum ta mai da su saniyar ware.

Wannan lamari dai ya sa an fara tunanin anya kuwa samun 'yancin Sudan ta Kudu ba zai haifar da karin rikici a yankin Darfur domin neman yanci ba?