Ana ci gaba da shagulgula a Juba

Shugaba Salva Kiir da shugaba Omar al Bashir Hakkin mallakar hoto AFP

Shugabannin kasashen duniya sun taya janhuriyar Sudan ta Kudu murnar samun 'yancin kai a yau.

Shugaba Obama na Amurka ya ce abune mai yuwuwa bayan shafe shekaru ana yaki a wayi gari da sabon farin ciki.

Dubban 'yan kasar ne suka taru domin yin shagulgulan samun 'yancin kan Sudan ta kudu.

Gwamnatin Sudan tace ta amince da Sudan ta Kudu a matsayin 'yantattar kasa.

Amma kuma ta jadda cewa 'yan Sudan ta kudu dake Sudan zasu rasa 'yan su na zama 'yan kasa.

Ana ganin cewa haryanzu da sauran runa akaba saboda takaddamar da akeyi akan yankin Abiye.