Idan an jima Gwamnati za ta yi taro da 'yan adawar Syria

Idan an jima a yau ne ake sa ran Gwamnatin Syria za ta bude wata tattaunawa a Kasar domin mayar da martani kan watannin da aka kwashe ana zanga zangar nuna kyamar Gwamnatin Shugaba Assad.

Gwamnatin ta bayyana cewa taron kwanaki biyu da za ta yi a birnin Damascus, zai hado kan Jamiyyyar Baath mai mulkin kasa da kuma masu adawa da ita wuri daya.

Wadansu majiyoyi daga Syria sun bayyana cewa taron zai samu halartar akalla mutane dari biyu cikinsu kuwa har da wakilan jam'iyyar Baath da kuma mukarrabanta, tare kuma da 'yan adawar da suka hada da masu zaman kansu da 'yan boko da kuma matasa masu fafutuka.

Ana kuma gab da tattauna batun shigo da tsarin Jamiyyu fiye da daya tare da fito da sabbin dokokin aikin Jarida a Kasar ta Syria.

A lokacin da Shugaba Bashar Al Assad ya bayyana gabatar da wannan taron tun a watan da ya gabata, ya ce yana so ne a samun cikakken tsarin da zai tabo bukatu daban daban na al'ummar Kasar.

Sai dai Wakilin BBC a can ya ce mahimmancin tattaunawar za ta dogara ne akan irin rawar da wakilan 'yan adawa za su taka.

A wata zanga zanga da 'yan Kasar suka yi ranar Juma'ar da ta gabata, sun bayyana cewa su sam babu wata tattaunawa da za'a yi da su.