Sojoji sun fatattaki 'yan jarida a Maiduguri

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin jihar Borno dake arewacin Najeriya na cewa an sake samun tashin wani bom da safiyar yau a kusa da dandalin Ramat dake tsakiyar birnin.

Wannan kuwa yazo sa'o'i goma sha biyu da tashin wani bom a unguwar Kaleri a daren jiya, wanda yayi sanadiyyar jikkkatar wasu jami'an soja da fafaren hula.

Kuma a daran jiya jami'an tsaro sun rika bi gida gida suna kashe mazaje suna kona gidajensu da motocinsu, bisa zargin basa basu hadin kai wajen zakulo 'yan kungiyar boko haram.

Abinda ya sa mazauna unguwar ke ta ficewa suna barin unguwannin.

Sai dai kuma rundunar tsaron hadin gwiwar ta JTF da aka kai birnin na Maidugurin cewa tayi ta samu nasarar kashe kimanin yayan kungiyar ta Boko Haram goma sha daya lokacin da ta kai samamen na daren jiya a unguwar ta Kaleri.

Wakiliyar BBC ta ce sojoji sun fatattakesu a lokacin da suka je unguwar ta Kaleri, domin ganewa idanunsu abinda ya faru