Yau aka rufe kamfanin jaridar NOW

Rupert Murdoch, mai kamfanin jaridar NOW Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Rupert Murdoch, mai kamfanin jaridar NOW

Mamallakin Kamfanin jaridar News of the world, Rupert Murdoch, ya isa Birtaniya don shawo kan matsalolin da ke kara bayyana, sakamakon abun kunyar nan na satar bayanai da ya dabaibaye jaridar.

A yau ne aka rufe gidan jaridar bayan da ta bayyana cewa wasu ma'aikatanta sun saci bayanai da sakonnin wasu ta waya.

Shugaban Jamiyyar adawa ta Lebo yayi kira ga Mista Murdoch da ya dakatar da yunkurin sa na mallakar gidan telbijin na B-sky-B har sai an kammala bincike kan abun kunyar da faru.