Wani bam ya tashi a Obalande dake Kaduna

Mutane kusan 16 aka ce sun samu raunuka a sakamakon wani bam da ya tashi a Unguwar Obalende a cikin garin Kaduna a daren jiya.

Wadanda abun ya faru akan idanunsu sun ce babu wanda ya ransa ransa.

Wannan Bam ya tashi ne yan sa'o'i kadan bayan tashin wani a Suleja, wani gari dake bayan Abuja babban birnin Najeriya, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane uku, tare da jikkata wasu bakwai.

Kawo yanzu dai rundunar yansanda ta Jihar Kaduna ba ta ce uffan game da lamarin.

A kwanan baya dai an sha samun tashe tashen Boma bomai a Kaduna, tare kuma da kuma gano wasu kafin su tashi.