Amurka ta dakatar da taimakon soji ga Pakistan

Sojojin Pakistan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin Pakistan

Gwmantin Amurka tace zata takatarda wani kason taimakon da sojin da take baiwa kasar Pakistan daya kai dala miliyan dari takwas.

A cewar Jagoran ma'aikata a fadar white House daukar matakin yazama dole

"Yace Pakistan babbar kawa ce a yakin da ta'adanci kuma ita tayi fama da tadananci, amma yanzu gaskiya suna wasu tajke taken da suka sa dole muka takatadda taimakon muke baiwa sojin su."

Wata jaridar Amurka ta ruwaito cewa Washington ta Fusata ne saboda Pakistan ta kore darakrun Amurka dake bada horo a kasar.