Bam ya kashe mutane uku a Suleja

A Najeriya, akalla mutane uku ne suka mutu, sannan wadansu suka jikkata a garin Suleja da ke jihar Naija sakamakon tashin da wani abu da ake zaton bam ne ya yi a harabar wata Coci da ke garin.

Wadanda suka shaida abun sunce fashewar ta auku ne da goshin la'asar kuma karar fashewar ta razana mutanen a yankin.

Hukumomi dai sun tabbatar da aukuwar fashewar, sai dai sun kara da cewa babu wanda ya mutu, illa dai an samu wadanda suka jikkata.