Al-Bashir ya yi gargadi akan yankin Abyei

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Omar Al-Bashir na kasar Sudan

Shugaba Omar Al-Bashir na Sudan ya bayyana cewa yankin Abyei mai fama da takaddama ka iya zama musabbabin rikici da sabuwar 'yantarciyar Sudan ta Kudu.

"Yanki Abyei na cikin Sudan, kuma dolene a bata martabar da ta kamata." In ji Al-Bishir kamar yadda ya shaida wa BBC bayan kaddamar da subuwar kasar Sudan ta kudu.

Shugaba Al-Bashir ya kuma nuna rashin jindadin sa ga yanayin da kasashen biyu suka tsinci kansu a yazu wadda hakan ya kai ga rabuwar kasar.

Sabuwar kasar Sudan din dai ta dauki sama da shekaru goma tana fafutuka da gwagwarmayar yankewa daga tsohuwar kasar Sudan wadda hakan ya haifar da salwantar sama da rayuka miliyan daya da rabi.

A wani hira dayayi da BBC, Shugaba Al-Bashir, ya kara da cewa ya so da kasar Sudan ta ci gaba da zama kasa daya, amma tunda muradun jama'ar yankin sun nuna suna son 'yanci, hakan shine mafi alheri ga kasar don hana tada rikici tsakanin bangarorin biyu.

Bayan da BBC ta tabayeshi ko shin yana ganin nan gaba za'a sake samin rashin jituwa a tsakanin su, sai shugaba Al-Bashir ya kada baki yace 'yankin nan ta Abyei da kowace bagare ke hasashen mallaka itace badakalar dake tsakinin su.