Rupert Murdoch na fama da karin matsin lamba

Rupert Murdoch Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kamfaninsa ya nemi sanin kwakwaf a kan Mr Gordon Brown

Hamshakin attajirin nan, mai kafafen yada labarai, Rupert Murdock, na fuskantar karin matsin lamba, yayin da ake samun karin zargin aikata ba daidai ba, kan wasu 'yan jaridar dake masa aiki a kamfanin yada labaransa na News International Corporation.

Daga cikin sabbin zargin da ake yi har da wanda ke nuna cewa jaridar News of the World ta biya wani jami'in tsaro na 'yan sanda mai aiki a fadar sarauniya wasu kudade, domin ya samo ma ta lambobin 'yan gidan sarautar Birtaniya.

Wakiliyar BBC ta ce, wani bincike da BBC ta gudanar ya gano wasu shaidu da ke nuna cewa jaridar Sunday Times ta rika binciken sanin bayanai na kwakwaf a kan tsohon Firaministan Birtaniya, Gordon Brown.

News International ya ce zai binciki wannan zargi.

Wannan abin kunya da ya dabaibaye katafaren kamfanin yada labarai na Rupert Murdoch yana da tasiri ta fuskar siyasa.

Dukkan manyan jam'iyyun siyasa biyu na Birtaniya sun rika zawarcin jaridun Mr Murdoch a 'yan shekarun da suka wuce.

Yau muhawara ta kaure a majalisar dokoki, inda 'yan adawa suka rika tashi daya bayan daya suna neman sai Firaminista David Cameron ya yi bayani a kan dalilan da suka sa shi daukar tsohon editan News of the World, Andy Coulson a matsayin mashawarcinsa kan harkokin yada labarai.

A makon jiya ne 'yan sanda suka kama Mr Coulson din, a binciken da suke gudanarwa kan zargin keta haddin jama'a ta hanyar shiga wayoyinsu don saurare ko karanta sakonni, da kuma biyan 'yan sanda kudade da suka saba ka'ida.