Afghanistan: An kashe dan uwan Karzai

Image caption Dan uwan karzai, Ahmad Wali Karzai

A Afghanistan, an bindige har lahira kanin shugaban kasar Hamid Karzai a birnin Kandahar.

Ana yi wa Ahmad Wali Karzai kallon daya daga cikin 'yan siyasa masu karfin fada a ji a kudancin Afghanistan.

Babban jami'in tsaronsa da suka dade tare, shi ne ya kashe shi, kafin sauran masu tsaron lafiyarsa su kuma su kashe mutumin.

A baya dai Ahmad Wali Karzai ya sha tsallake rijiya da baya, a yunkurin halaka shi.

Shi ne shugaban majalisar lardin Kandahar.

Ya dai sha musanta zargin da ake masa na fataucin miyagun kwayoyi, da kuma cin hanci.