Shari'ar kisan shugaban Boko Haram

Image caption Jami'an 'yansanda a Nigera

A Najeriya an fara shari'ar jami'an 'yan sanda hudu da ake zarginsu da kashe shugaban Boko Haram a shekarar 2009 a karon farko a bainar jama'ar a wata kotu a Abuja.

Alkalin kotun dai ya dage saurarran karar zuwa ranar 19th ga watan Yuli, domin bukatar da lauyan gwamnati ya nuna da kara yawan wadanda ake tuhuma da hannu a kisan.

An dai tsaurara matakan tsaro a harabar kotun a lokacin da ake gudanar da shari'ar.

An dai kama Shugaban kungiyar ne Mohammed Yusuf da ransa kuma aka dauki hotunansa, amma daga baya sai aka tsince gawarsa, inda akayi mishi ruwan harsasai.

Dama dai an fara wannan shari'ar ne a wata kotun tarayya dake Kaduna, amma daga baya sai aka maida shari'ar reshenta da ke Abuja.

Batun gurfanar da wadanda ake zargin na daga cikin jerin bukatun da`yan kungiyar boko-haram din suka dade suna cewa sai sun samu biyan muradi kafin su daina kai hare-haren da suke ikirarin kaiwa.

Hakazalika kungiyar Dattawan jihar Borno ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta janye jami'an sojojinta daga Maiduguri.

Kungiyar dai ta bayyana hakan ne bayan taron da tayi da yammacin jiya, inda ta zargi sojojin da cin zarafi da kuma kashe wadanda basu jiba basu gani ba.

Sai dai rundunar hadin gwiwar Samar da tsaron ta JTF, ta musanta dukkannin zargin da ake yiwa jami'an nata a wata sanarwar da ta fitar, ita ma da marecen na jiya.