Matsalar fari a gabashin Afrika

Image caption Wasu na cin abinci a wani sansanin yan gudun hijira

Manyan kungiyoyin samar da agaji na Birtaniya na shirin fadada ayyukansu a kasar Somalia domin taimakawa wasu daga cikin mutane miliyan goma dake fuskantar barazanar yunwa a gabashin nahiyar Afrika.

Yankin dai na fama da matsanancin fari, sai dai kungiyoyin agaji sun rika fuskantar tarnaki sakamakon rashin tsaro a Somalia inda babu wata cikakakiyar gwamnati a shekaru ashirin da suka wuce.

Kwamitin kai dauki gagagawa na bala'oi ya ce Somalia na daya daga cikin wurare masu matukar wahala wurin samar da agaji.

Bugu da kari da dama daga cikin kungiyoyin samar da agaji na kasa da kasa an haramta masu aiki a wuraren dake karkashin ikon kungiyar islama ta al-shabab, da ake ganin tana da alaka da kungiyar alqaeda.

A makon da ya wuce ne kungiyar al-shabab tayi shellar cewa zata dage takunkunmi data sanyawa kungiyoyi samar da agaji na kasashen waje biyo bayan fari mai tsanani da ake fuskanta.

Akan haka ne kungiyoyin a yanzu ke neman hanyoyin taimakawa jama'ar Somalia dake kudancin kasar, duk da cewa sabbin shiryen -shiryen da akayi da kungiyar alshabab din kawo yanzu ba'a fara aiki dasu ba.