'News of the World na hulda da gungun masu aikata manyan laifuka'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tsohon Pira Ministan Burtaniya, Gordon Brown

Tsohon Pira Ministan Burtaniya, Gordon Brown ya yi zargin cewa akwai alaka tsakanin Kamfanin Jaridar Rupert Murdoch na News of the World da wasu gungun masu aikata manya laifuka.

Tsohon Pira Ministan dai ya yi kira da a binciki bangarorin biyu.

A ranar litinin ne dai rohatanni suka fito wanda ke nuni da cewa jaridar Sunday Times wanda Mista Murdoch ya mallaka ta biya wasu mutane kudi domin samun bayanai akan tsohon Pira Ministan wanda kuma ba bisa kan ka'ida ba.

Wannan batu dai na daya daga cikin abun kunyan da ake zargin wasu daga cikin kafofin yadda labaran da Mista Murdoch ya mallaka da aikatawa.

Da yake magana da BBC, Mista Brown ya zargi jaridar News International da hulda da gungun masu aikata manyan laifuka, amma yaki ya bada karin haske akan lamarin.