Kusurwar Afirka: kowa na kokarin kai labari

Image caption Fari yasa mutane na kaura a kusurwar Afirka

"Wannan kokari ne na ko a mutu, ko a yi rai," inji Weheleey Osman Haji, wacce kwana guda kenan bayan ta haihu a garin Liboi na kan iyakar Kenya.

Ita da 'ya 'yanta biyar sun kwashe makonni suna takowa a kafa zuwa Kenya tun daga kasar Somalia, wacce saboda rikicin da take fama da shi zata iya shawo kan farin mafi muni cikin shekaru sittin da kasashen na kusurwar Afurka ke fuskanta.

Ita dai Weheeley ta sanya dan na ta sunan Iisha, wanda ke nufin 'rayuwa'.

Jaririn yana barci ne akan kafadar mahaifiyarsa, bai ma san halin da ake ciki ba, yayin wannan hira da BBC, kuma

An haife ta ne a gindin bishiya, a wurin da nisan kilomita 80 daga arewacin sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab dake kasar Kenya inda a kullum dubban 'yan kasar Somalia ke tururuwa bayan tafiya mai matukar wuya.

Sun dai tsallaka iyaka ne da fatan zasu samu sauki, amma kuma wasu 'yan gudun hijirar basu ma san iya tsawon tafiyar da zasu yi ba kafin su isa sansanin na Dadaab.

"Akwai fari, kuma mun yi tafiyar kwanaki 22, muna shan ruwa kawai, inji Malama Haji.

Ta kuma ce, "Tun da na haihu ban ci komai ba."

"Yanzu dai ina bukatar abinci, da ruwa da kuma muhalli- da ma dukkan abubuwan da dan adam ke bukata.

A wannan wuri dai akwai mata iyaya da dama kamar Haji. Kuma daya daga cikin iyaye matan tace, ta bar jaririnta a bakin hanya saboda ba zai jurewa tsawon tafiya zuwa sansanin 'yan gudun hijiran dake Kenya ba.

Saboda yara kanana sun yi ma ta yawa, ta jefar da jaririn a cikin hamada.

Ta kuma ce, "har yanzu idan jaririn da na jefar na cikin zuciya ta.

Ita ma Rukiyo Maalim Noor ta kwashe kwanaki ashirin tana tafiya, kuma tana da jariri dan wata guda.

Tace, "Dole muka gudu. Ba zamu zauna ba saboda fari. Ba abinci, babu wani abu a za'a baiwa yara"

Yawancin 'yan Somaliyan sun shiga Kenya ne ta garin Liboi dake kan iyaka. Sai dai kuma wasu da dama sun yi ta ke ta daji ne kawai saboda suna tsoron kada jami'an tsaro su hana su shiga Kenya.

Gwamnati dai ta rufe kan iyakar Kenya da Somalia ne a farkon shekara ta 2008, saboda tashin hankalin da ake yi a Somalia, inda yanzu haka masu tsarin ra'ayin Islama suke rike da iko a yankin tsakiya da kuma kudancin kasar.