Kungiyar human rights watch ta zargi yan tawayen Libya da sata

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani dan tawaye a kasar Libya

Kungiyar kare hakkin bilAdama ta Human Rights Watch ta zargi 'yan tawayen Libya da sace sace, da lalata kayan gwamnati da kuma cin zarafin fararen hula a garuruwanda suka kama a yammacin kasar.

Masu sanya ido na kungiyar dake birnin New York, sun ce sun shaida al'amarin da idanunsu, kuma sun yi hira da wasu da suka shaida lamarin.

Sun ce yan tawayen na Libya sun kona gidajen mutane da suka sace kayayyakin dake ciki da shaguna da asibitoci sannan suka lakadawa mutanenda suke zargin cewa magoya bayan gwamnati ne dukan tsiya.

Birane da wanan abun ya shafa sun hada da al-Awaniya, Rayayinah, Zawiyat al-Bagul da al-Qawalish wadanda 'yan tawayen suka kama a watan jiya.