An rufe jami'ar Maiduguri saboda rashin tsaro

Image caption Mutane da dama na kaura daga birnin Maiduguri

A Najeriya, yanzu haka daliban Jami'ar Maiduguri sun tattara komatsan sun fita daga harabar makarantar.

Wannan kuwa ya biyo bayan sanarwar rufe makarantar ne da Hukumar Gudanarwar Jami'ar ta fitar da yammacin jiya.

Mutane 3 ne suka mutu wasu da yawa suka jikkata a yau a lokacin da wani abu ya fashe a kusa da wani wurin duba ababen hawa na soji a Maiduguri.

Hukumar ta ce ta dauki wannan mataki ne domin kare lafiya da rayukan daliban, sakamakon kalubalen tsaron da ake ci gaba da fuskanta a birnin Maiduguri da ma wasu sassan jihar Borno.

Hukumomi dai sun dora laifin lamarin a kan kungiyar nan da ake kira Boko Haram.

Rufe Jami'ar ta Maiduguri dai na zuwa ne a daidai lokacin da mazauna birnin da dama ke ci gaba da yin kaura zuwa wasu jihohin.

Yanzu haka dai kanana da manyan tashohin mota na ta samun karin matafiya.

Mazauna birnin Maidugurin dai na kokawa ne da matsalar yawan hare haren bama bamai da na bindigar da ke ci gaba da faruwa a unguwannin nasu.

Abinda kuma ke sa suna fuskantar fushin jami'an sojin da suke zargin na cin zarafi da hallaka wadanda basu ji ba su gani ba.

Sai dai Rundunar hadin gwiwar samar da Tsaron ta musanta ta ce, wannan zargi ne.

Rundunar tace galibin mazauna birnin ba sa ba su hadin kai wajen gudanar da binciken masu kai hare haren da take zargin, saboda suna tare da su ne.