An sami faduwar darajar kudin euro

Yau kasuwar hada-hadar kudi a Turai ta kasance mai tambal tambal.

A wani lokaci, sai da takardar kudin euro ta yi faduwar da ita ce mafi girma cikin watanni hudu a kan dalar Amurka.

Hakan na faruwa ne ga kasuwannin kudin, sakamakon yadda ministocin kudi na tarayyan turan suka gaza amincewa da yunkurin baiwa kasar Girka wani karin kudaden tallafi.

Olli Rehn shi ne ministan harkokin kudi na tarayyar turai, ya kuma ce babban kalubalen dake gaban su shi ne su shawo kan wannan matsala ta bashi, wanda hakan zai kare farfadowar tattalin arziki da ake samu a Turai, da samar da ayyukan yi.

Babbar fargabar da ake yi ita ce matsalar na iya watsuwa zuwa kasashe irin su Italiya da Spain.