Dan majalisar Amurka ya yi kira a binciki News Corporation

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rupert Murdoch shugaban kamfanin News international

A cikin wata sanarwa aka fitar a rubuce senata Jay Rockefella ya nuna damuwarsa akan cewa batun satar bayanan wayoyin salula da ake zargin 'yan jaridar kamfanin News corporation da yi, me yuwa ya shafi wasu a Amurka, ciki harda da mutanen da hare haren ranar goma sha daya ga watan satumba ya shafa .

Shugaban kwamitin kasuwanci na majalisar dattawan Amurka Jay Rockefeller, ya ce zai baiwa hukumominda suka dace umurnin su gudanar da bincike kan manema labarun News Corporation don tantance ko sun karya dokar Amurka.

Senatan ya yi gargadi a'kan ilolin da hakan zai haifar muddin aka samu wata shaida dake nuni da cewa kamfanin ya sabama dokar kasar

Kamfanonin yadda labaru da Mr Murdoch ya mallaka a Amurka sun hada da mujallar Wall street da kuma Fox news