Takkadama kan 'yan gudun hijira a Kenya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sansanin 'yan gudun hijira a Kenya

Gwamnatin kasar Kenya ta shaida cewa tana bukatar a baiwa 'yan kasar Somalia agajin abinci don rage kwararar duban 'yan kasar zuwa cikin kasar ta.

Sansanin 'yan gudun hijar ta Dabaab da ya cika ya batse, dake Arewa maso gabashin Kenya.

Sansanin dai ya kasance gida ga 'yan gudun hijira sama da dubu dari uku da tamanin ayayinda dubu daya da dari hudu ke kwararowa a kowace rana.

Kasashen duniya sunyi kira da a bude sabuwar sanssani a yankin, amma gwamnatin kasar Kenyar na dari dari yin haka.

Gwamnatin kasar Kenyar dai na kokarin rage kwararowar 'yan gudun hijirar kasar Somalia zuwa kasar ta ne.

Mataimakin Ministan tsaro cikin gida Kenyar, Orwah Ojedeh ya shaida cewa ba bude sabon sansani bane kusa da Dabaab zai shawo kan matsalar.

A cewar sa samar da ishassen cimaka cikin Somalia ne zai kawo karshen matsalar don yunwa ce ke adabar jama'ar, ba matsalar tsaro bane ya sanya galibin 'yan gudun hijirar ke fitce wa daga kasar.

Hukumar samar da binci na Majalisar Dinkin Duniya ta shaida cewa tana iya kokarin ta na ganin ta inganta samar da abinci a kasar Somaliya amma fa banda yakunan dake karkashin kungiyar nan ta Al Shabab sai dai in har kungiyar ta bada tabbacin tsaro.

A watanni sha takwas da suka gabata ne Hukumar samar da abincin ta fice daga yankin a sakamakon baraza ga rayukan ma'ikatan ta.

A makon daya gabata ne kungiyar Al Shabab ta cire takunkumin da ta sanya wa ma'ikatun agaji na kasashen waje.