Murdoch: "Na fasa sayen BSkyB"

Mutumin da ya mallaki kamfanin jaridar News of the World, Rupert Murdoch ya ce ya janye aniyarsa na sayen BSKYB.

Kamfanin na ta fuskantar matsin lamba na ya dakatar da batun sayen gidan talabijin din, bayan da ta fito fili cewa ma'aikatansa na da hannu wajen satar shiga wayoyin wasu manyan mutane domin samun bayanai.

Praminista Birtaniya David Cameron ya bada sanarwar cewa, za a bai wa kwamitin binciken da za a kafa mai zaman kansa game da zargin satar shiga wayoyin jama'a domin karanta ko sauraron sakonni, ikon gayyatar masu gidajen jarida , da 'yan jaridar, da 'yan sanda da kuma 'yan siyasa su bayyana a gabansa, domin bada shaida a bainar jama'a, bayan sun yi rantsuwa.