Rudunar sojin Nigeria ta maida martani

Image caption Wani jami'in soja a Nigera

A Najeriya, Rundunar sojin kasar ta maida martani dangane da kiraye kirayen da wasu 'yan siyasa da masu fada aji a jihar Borno suka yi na neman a janye sojoji daga jihar, biyo bayan zargin da ake wa sojojin da cin zarafin jama'a.

Hakazalika rahotanni sun ambato wani kakakin kungiyar ta Boko Haram na cewa ba zasu tattauna da gwamnatin kasar ba, matukar gwamnatin bata janye sojojin ba.

To sai dai kakakin rundunar sojin Najeriyar Laftanan Kanar Raphael Isa, a wata hira da BBC ya ce kuskure ne a rika bayyana cewa sojoji na muzgunawa jama'a.

Ya kuma bayana kiraye kirayen a matsayin wani abun takaice kuma acewarsa lamarin 'da be kai haka ba da tun farko kwamitin dattawan jihar yasa baki don magance matsalar.

Laftanan Isa ya ce ba yanzu ne lokacin da ya kamata a ce an janye sojoji ba , za'a iya haka ne idan an samu wata mafita.