Shari'ar 'yan sandan da suka kashe shugaban Boko Haram

Image caption Ana zargin 'yan sanda da yiwa shugaban kungiyar Boko Haram, Mohammed Yusuf, kisan gilla.

Jami'an 'yan sandan hudu da ake zargi da hannu wajen kisan gillar shugaban kungiyar nan da akafi sani da Boko Haram, Mohammed Yusuf da wasu magoya bayansa, sun hallara cikin farin kaya a zaman babbar kotun tarayyar Najeriyar da akayi a birnin Abuja.

A yayin zaman kotun, lauya mai gabatar da karar Mr. Ojabor ya nemi kotun wanda alkali Dunatus Okorowo ke jagoranta ta ba shi izinin hade karar 'yan sanda hudu da ake zargi da aikata kisan gillar wato ACP J.B Abang da ACP Akeera da CSP Mohd Ahmadu da ACP Mada buba, da kuma sabuwar karar da ake tuhumar dan sanda sajent Adamu Gado wanda shima ya bayyana a gaban kotun.

Mai gabatar da karar dai ya shaidawa kotun cewa yana bukatar yin hakan ne domin tuhumar da akewa sajent din da kuma shaidun da za su gabatar duka daya ne da na sauran hudun da aka shigar da kararsu da fari.

Abinda lauyan dake kare sajent Adamu Gado Mr. Edwin Enegedu da jagoran lauyoyin dake kare sauran 'yan sandan hudu, Mr. Paul Erokoro suka amince da shi.

Dage shari'a

Hakan ne ya sa alkalin kotun ya dage shari'ar zuwa ranar 19 ga watan da muke ciki don gabatar da haddadiyar karar a gaban kotun tare da ci gaba da sauraron karar.

Sajent Adamu Gado dai na cikin jerin sunayen wadanda ake tuhuma da hannu a zargin aikata kisan gillar, amma aka cire sunansa, kuma a yau aka sake neman maida shi cikin jerin wadanda ake zargin.

Image caption Wasu daga cikin jami'an 'yan sandan da ake tuhuma sun boye fuskokinsu.

Lauyoyi dake kare wadanda ake zargin dai basu yarda sunyi magana da 'yan jarida ba.

Zaman kotun dai anyi shi ne cikin tsauraran matakan tsaro, inda aka baje 'yan sanda wasu a motocin sintiri da kuma jami'an tsaro na farin kaya a wajen kotun.

Haka kuma an hana ajiye ababen hawa a wajen kotun kuma duk wanda zai shiga harabar kotun sai da aka caje shi da kyau kafin barinsa ya shiga.

A ranar 23 ga watan fabrairun shekerar da mu ke ciki ne dai aka fara shigar da karar da ake tuhumar 'yan sanda hudu a gaban wata kotun tarraya dake jihar Kaduna, inda daga bisani aka dawo da ita gaban wannan kotun ta Abuja wacce ta bada belinsu a ranar ashirin ga watan Aprilun da ya gabata.

Ana dai zargin 'yan sandan ne da aikata lafin ta'addaci wanda kuma ya sabawa dokokin manyan laifuka na kasa.

A ranar 30 ga watan Yulin shekarar dubu biyu da tara 'yan sanda suka yiwa shugaban Boko Haram, Mohammed Yusuf, kisan gilla.

Dattawan Borno

Gwamnatin jihar borno dai ta bukaci jami'an tsaron da ke aikin tabbatar da tsaro a jihar da su rinka yin taka tsan-tsan wajen gudanar da ayyukansu ba tare da keta hakkin biladama ba.

Gwamnatin ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwar da ta fitar dangane da yanayin tsaron da ake ciki a Jihar.

A bangare guda kuma Kungiyar Dattawan Jihar Borno ta yi kira ga Gwamnatin tarayya da ta janye sojojin daga birnin, bisa zargin da ta ke na cewar suna cin zarafi da kashe wadanda ba su jiba basu gani ba.

Sai dai Rundunar Hadin Gwiwar Samar da Tsaron - JTF -- ta musanta dukkanin zargin da ake yiwa jami'anta a wata sanarwar da ita ma ta fitar ga manema labarai.

Rufe jami'a

Yanzu haka daliban Jami'ar Maiduguri sun tattara komatsan sun koma gida.

Wannan kuwa ya biyo bayan sanarwar rufe makarantar ne da Hukumar Gudanarwar Jami'ar ta fitar.n jiya.

Hukumar ta ce ta dauki wannan mataki ne domin kare lafiya da rayukan daliban, sakamakon kalubalen tsaron da ake ci gaba da fuskanta a birnin Maiduguri da ma wasu sassan jihar Borno.

Image caption Jama'a da dama na kaura daga birnin Maiduguri saboda tabarbarewar tsaro.

Hukumomi dai sun dora laifin lamarin a kan kungiyar nan da ake kira Boko Haram.

Rufe Jami'ar ta Maiduguri dai na zuwa ne a daidai lokacin da mazauna birnin da dama ke ci gaba da yin kaura zuwa wasu jihohin.

Yanzu haka dai kanana da manyan tashohin mota na ta samun karin matafiya.

Mazauna birnin Maidugurin dai na kokawa ne da matsalar yawan hare haren bama bamai da na bindigar da ke ci gaba da faruwa a unguwannin nasu.

Abinda kuma ke sa suna fuskantar fushin jami'an sojin da suke zargin na cin zarafi da hallaka wadanda basu ji ba su gani ba.