Sudan ta Kudu na shirin samun wakilci

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya bada shawarar a amince da kasar Sudan ta Kudu, ta samu wakilci a majalisar, lamarin da zai sa ta zama kasa ta dari da casa'in da uku, a majalisar dinkin duniyar.

Ministan harkokin wajen Jamus kenan, Guido Westerwelle ke cewa, a madadin wakilan kwamitin tsaro, ina taya Jamhuriyar Sudan ta Kudu murna kan wannan abin tarihi.

Nan zuwa gobe Alhamis ake fatan za a kammala shirin shigar da kasar ta Sudan ta Kudu, cikin majalisar, bayan wata kuri'a da zauren majalisar zai kada.