Gwamnatin Nigeria zata aikewa mutanen Maiduguri kayan agaji

wasu mazauna  Maiduguri
Image caption wasu mazauna Maiduguri

Gwamnatin tarraya a Nigeria ta ce zata aikewa mutanen Maiduguri agajin abinci da wasu abubuwan don rage kuncin da suke fuskanta.

Hakan ya biyo bayan wata ganawa da 'yan majalisun dokokin tarraya daga jihar Borno suka yi ne da shugaba Goodluck Jonathan don nemo hanyar warware matsalar. Daruruwan jama'a ne dai ke ficewa daga muhallansu a Maidugurin sakamakon tabarbarewar tsaro a garin.