Hotunan ramukan binne mutane a Kordofan

Image caption Hotunan ramukan da aka binne mutane

Wata tawagar Amurkawa dake sa ido, ta fitar da wasu hotuna da tace sun nuna shaidar ramukan da aka binne mutane da dama a yankin Kordafan dake Sudan.

Ana dai fada ne tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawaye a yankin. Kungiyar wadda tauraron cinima na Hollywood, Goerge Cloony ya kafa, ta ce abubuwan da ta gani da kuma rahotanni daga wadanda suka ganewa idanunsu sun nuna wasu wurare uku da aka binne sama da mutane dari a Kadugli , babban birnin jahar Kordafan.

Wakilin BBC ya ce mai magana da yawun dakarun gwamnatin Sudan din ya shaidawa BBC cewa ba gaskiya ba ne kuma ba'a kashe fararan hula a Kadugli. Mahukuntan Sudan dai sun ce yakin da suke da masu tada kayar bayan yankin halattace ne.