Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka, FBI, zata binciki kamfanin News Corporation na Rupert Murdoch

Rupert Murdoch Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rupert Murdoch

Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka ta FBI, ta ce ta fara wani bincike kan zarge zargen cewa, kamfanin News Corporation na Rupert Murdoch, ya nemi ya saci hanyar sauraro da kallon sakonnin wadanda harin sha daya ga watan Satumba ya shafa.

Hakan ya biyo bayan wata bukatar 'yan siyasar Amurka ne ta yin bincike biyo bayan rikicin da ake yi a Burtaniya saboda satar sauraro da kallon sakonnin jama'a wanda kamfanin jaridar Murdoch ya yi.

Wani dan majalisa Peter Kin ne ya rubutawa kumar binciken manyan laifukan wasika yana bukatar ta da tayi bincike.