'A matsawa 'yan siyasa lamba' -Obama

Shugaba Obama Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Obama

Shugaban Amurka, Barrack Obama ya yi kira ga Amurkawa da su kara matsin lamba kan 'yan siyasar kasar domin warware kiki-kakar siyasar da aka samu kan gibin kasafin kudin kasar.

Shugaba Obama ya ce lokaci na kurewa, kuma kasar zata iya rasa matsayinta na kasa mai daraja ta taya a ma'aunin bayarda da bashi.

Ranar biyu ga watan Ogusta ne dai wa'adin kara irin bashin da kasar zata iya ciwowa.