Bama bamai biyu sun tashi a Maiduguri

Image caption Birnin Maiduguri dai na fuskantar hare-hare a 'yan kwanakin nan.

A Najeriya, bama-bamai biyu sun tashi kusa da wani sha tale-tale a unguwar Bulunkutu dake birnin Maiduguri, inda ya raunata 'yan sanda bakwai da safiyar yau.

Shugaban rudunar tsaron ta hadin gwiwa, Manjo Janar Jack Okechukuwu Nwago, wanda ya tabbatarwa BBC da aukuwar lamarin ya ce bama baman biyu sun tashi ne da misalin karfe 7.16.

Sai dai mazauna unguwar ta Bulunkunta suna ficewa daga gidajensu, inda suke fargabar cewa sojoji za suyi ramuwar gaiya akan su.

Rahotanni dai daga yankin na cewa an tsaurara matakan tsaro a unguwar kuma ana bi gida gida an neman 'yan kungiyar Boko Haram wadanda ake kyautata zaton sune suke kai harin.

Har wa yau dai wata kungiyar dattawa a yankin ta yi kira ga gwamnatin tarraya da ta janye sojoji a jihar saboda abun da ta kira cin zarafin jama'a da kuma rura rikici a yankin.

Rudunar tsaron ta hadin gwiwa dai ta musanta hakan inda ta zargi dattawan da kuma mutanen garin da nuna goyon baya ga kungiyar ta Boko Haram.