An bukaci Firaministan Guinea Bissau ya yi murabus

Image caption Firaministan Guinea Bissau

Dubban jama'a ne suka gudanar da zanga zanga a kasar Guinea Bissau dake yammacin Afrika inda suka bukaci firaministan kasar Carlos Gomez Junior da yayi murabus.

Masu zanga zangar dai sun bayyana cewa gwamnatin kasar ta gaza wajen shawo kan matsalar tsadar rayuwa, tare da zargin cewa akwai tambayoyinda ya kamata gwamnatin tayi bayani akai game da kisan tsohon shugaban kasar Joe Bernardo Viera.

Wasu majiyoyi a kasar sun ce kimanin mutane dubu biyar zuwa dubu goma ne suka bazama akan tituna a babban birnin kasar inda suka gudanar da zanga zangar lumuna.

Sun yi kira ga firaministan kasar ya sauka daga mukaminsa sun kuma suna zarginsa da kisan tsohon shugaban kasar Joe Bernado Veira.