Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi ki yaye da BBC Hausa: Shayar da yara madara

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Shayar da jariri madara

Madara na daga cikin abincin dake sahun gaba-gaba da iyaye ke amfani da ita a matsayin abinci ga jariransu, musamman ga wadanda ba sa bin tsarin shayar da nono zalla na tsawon watanni shida duk kuwa da muhimmancin dake tattare da hakan.

To ko madara na maye gurbin nono uwa a wajen shayar da jarirai? Wakiliyar BBC Bilkisu Babangida dake Maiduguri a Najeriya ta duba mana wannan batu.

To a birtaniya duk da kokarin da hukumomi su ka ce su na yi na ganin iyaye mata sun rungumi tsarin shayar da nono zalla na tsawon watanni shida, wasu masana na ja da tsarin.

A watan Satumbar shekarar 2008 ne dai badakalar madarar mai dake da sinadarin mai guba na melamine ya barke a kasar sin.

Kuma madarar da dangoginta sun yi sanadiyyar mutuwar jarirai shida a kasar, yayinda hukumomin Sin suka ce matsalar ta kuma shafi wasu mutane kusan dubu dari uku.

A wancan watan da kuma watannin da suka biyo baya ne kuma kasashen nahiyar Turai suka hana shigar da madara da duk wasu dangoginta daga Sin.

Haka ma Amurka ta fitar da wani gargadi game da shigar da kayan da ake shigarwa kasarta daga kasar ta Sin saboda wannan annobar.

Ayi sauraro lafiya.