'Yan tawayen Libya sun samu daukaka

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Taro a kan Libya

Wasu kasashen duniya sun amince da Majalisar wucin gadi ta 'yan tawayen Libya a matsayin halastacciyar gwamnati.

A taron ministocin hulda kasashen wajen kasashen larabarawa, da kuma na yammacin Turai, Ministan hulda da kasashen wajen Italiya, ya shaidawa maneman labarai cewa, daga yanzu za'a rika daukar majalisar wucin gadi ta 'yan tawayen Libya a matsayin halastacciyar gwamnati.

Franco Frattini ya fadi hakan ne bayan ganawar da ministocin kasashen dake da ruwa da tsaki a lamarin na Libya inda kuma suka tattauna mataki na gaba da zasu dauka domin dakile dakarun Kanar Gaddafi.

Taron wanda aka yi a birnin Istanbul na Turkiyya ya kuma amince cewa, wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman akan batun na Libya Abdel Elah Al Khatib ya je birnin Tripoli domin gabatarwa Kanar Gaddafi sabbin ka'idojin tsaigata wuta: