An gano wata gonar tabar wiwi mafi girma a Mexico

Image caption kwayoyin wiwi da aka kwace a Mexico

Dakarun Mexico sun ce, sun gano wata gonar tabar wiwi mafi girma da aka taba ganowa a kasar.

Dakarun na sintiri ne a yankin Baja California,me nisan kilomita dari uku daga iyakar kasar da Amurka, inda suka yi kicibis da wata babbar gonar ganye wiwi da aka zagaye ta da kayoyi

Kwamandan rundunar sojin kenan janar Alfonso Duarte yake cewa, wannan gonar ganyen wiwin, itace daya daga cikin mafi girma da aka taba ganowa a Mexico wadda nan ba da jimawa ba za a lalata.

Wadda aka gano a baya mafi girma itace mai girman hekta dari da biyar dake Rancho de Bufalo, amma wannan girmanta ya kai hekta 120, don haka itace mafi girma a kasar nan.