Badakalar jaridar 'News of the World'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rupert Murdoch tare da Rebekah Brooks

Babbar shugabar kamfanin News International mallakar Rupert Murdoch, dake nan Birtaniya, Rabekah Brooks, ta ajiye aikinta.

Ta na ta shan suka dangane da batun satar sauraro da kallon sakwanni a wayoyin jama'a a jaridar News of the World, wadda ita ce editar jaridar har zuwa shekara ta 2003. Ana zargin jaridar da satar sauraro da kallo sakwaani a wayar dalibar nan da aka kase, Milly Dowler, a lokacin da Ms Brooks ke editar jaridar.

Ta dai musanta masaniya game da batun satar sauraro da kallon sakkwaanin wayoyin jama'a kuma oganta Rupert Madoch ya goyi bayanta dari bisa dari.

Baya ga amincewa ya rufe Jaridar nan ta News of the World, Yanzu daular hamshakin attajirin nan da ya mallaki kafofin yada labarai a kasashen daban daban, Rubert Murduch ya amince da murabus din babbar Jami'ar gudanarwa ta kamfaninsa na News International da ke nan Burtania, watau Rabekah Brooks.

Image caption Shugaban Jam'iyyar hammaya ta Labour, Ed Miliband

Tuni dai Firayi ministan Burtaniya, David Cameroon, yayi maraba da wannan labari, na cewar Rebekah Brooks ta yi murabus daga kan mukaminta, yana mai cewar wannan shine matakin da ya fi dacewa.

Sai dai Shugaban Jam'iyyar hamayya ta Labour, Ed Milliband, ya bayyana cewar ko da ya ke yayi marhabin da jin wannan labari, to amma yana ganin yanzu akwai sauran rina a kaba.

"Na yi farin-ciki cewar a karshe Rebekah ta dauki alhakin abun da ya faru a lokacin da ta ke rike da mukamin edita a Jaridar News of the World, kamar satar sauraren sakonnin da aka tura kan wayar Milly Dowler,"

"To amma kamar yadda na fada a lokacin da na yi kiran ta yi murabus kwanaki goma da suka wuce, wannan al'amari ba abu bane da ya shafi mutum guda shi kadai, wannan ala'amari na yadda baki daya wannan kamfani ya ke gudanar da aikinsa."

Ya ce a gani na kamata yayi ace Rebekah ta yi murabus tun ma farko.

Shi dai hamshakin attajirin da ya mallaki kamfanin, watau Rupert Murdoch ya bayyana cewar yayi imanin kamfaninsa na News Corporation ya tafiyar da wannan ala'mari yadda ya kamata.

A wata hira da yayi da mujallar Wall Street ta Amurka, wadda ita ma ta sa ce, Mr Murdoch ya ce kamfanin na News Corp, yayi abun da ya kira wani dan karamin kuskure, kuma nan bada jimawa ba zai farfado daga irin illar da ya fuskanta.