Majalisar wakilan Nigeria ta tattauna da kungiyar kwadago

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Majalisar dokokin Nigeria

A Najeriya, Majalisar wakilan kasar ta gayyaci shugabannin kungiyar kwadagon kasar, wadanda ke barazanar fara yajin aiki don duba yiwuwar shawo kansu.

Kungiyar dai ta baiwa gwamnati wa`adin mako guda domin ta fara biyan ma'aikatan kasar da sabon tsarin albashi mafi karanci na naira dubu goma sha takwas, tsarin da gwamnatin ta ce sai `yan matakin albashi daga shida zuwa kasa ne karin zai shafa, yayin da`yan kwadagon suka ce sai dai karin ya zama na bai daya.

Hon Isyaka Muhammad Bawa, na daga cikin mambobin da suka gana da wakilan kungiyar kwadagon kuma ya ce suna son a biyasu dukanin matakan , amma ya ce babu isashen kudi a cikin kasafin kudin kasar.

Sai dai ya ce sun bada shawarar cigaba da tattaunawa da kungiyar kwadagon domin ganin yadda al'amuran zasu kasance a kasafin kudin shekara me zuwa.

A nasu bangaren kuma mataimakin kakakin kungiyar kwadagon Comrade Nuhu Abbayo Toro ya ce ba gudu ba ja da baya dangane da yajin aikin gargadinda suka kudiri aniyar yi.