Anyi zanga zanga a Syria

Masu zanga zanga a Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga zanga a Syria

Rahotanni sun ce dubban mutane a Syria sun gudanar da zanga zangar kin jinin gwamnati, inda suka yi watsi da gargadin dakarun tsaro na kada a gudanar da zanga zangar.

Masu fafutukar kare hakkin bani adama sun ce an kashe mutane takwas da suka hada da uku a Aleppo da biyu a Homs.

Masu fafutukar sun ce dakarun tsaro sun bude wuta kan masu zanga zangar tare da harba hayaki mai sa kwalla a wurare da dama.

Wani mai kare hakkin bil'adama ya ce kalla mutane miliyan daya da dubu dari biyu ne su ka gudanar da zanga zangar a fadin kasar.