Gwamnan Jihar Borno yayi wa jami'an tsaro ahir

Gwamnan Jihar Borno a Najeriya, Kashim Shettima ya sake yin kira ga yan kungiyar Jama'atu Ahlis Sunna Lidda'awati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram da su ajiye makamansu domin shiga sasantawa don samun zaman lafiya a Jihar.

Gwamnan ya yi wannan kira ne a cikin wani jawabi da yayi wa al'umar jihar dazu a Maiduguri babban birnin Jihar.

Hakan kuma Gwamna Kashim Shettima ya yi kira ga mutanen da suke yi kaura daga jihar da su koma, su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Gwamnan ya bayar da tabbacin cewar gwamnati ta dauki matakai domin tabbatar da daidaituwar al'amura a jihar.

Tuni dai kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta zargi rundunar sojin Nigeria da aikata kisan ba rarrabewa a yakin da take yi da kungiyar 'yan gwagwarmayar Islaman nan a arewacin kasar.

Kungiyar ta Amnesty ta ce, ta yi imanin cewa mutane 25 ne, harda mata da yara aka hallaka a wani artabu da sojoji sukayi da 'yan boko haram mako guda da ya wuce.

Wannan dai ya ninka adadin da rundunar sojin ta bayar.

Wakilin BBC ya ce a watanni biyun da suka wuce a kara yawan dakarun da ake dasu arewa masu gabasin Nigeria, amma kuma harkar tsaro sai kara tabarbarewa ta ke yi.

Rundunar tabbatar da tsaro a yankin ta ce mutane na gama baki da kungiyar ta Boko Haram, abinda ke sa aikin sojin ya kara zama mai wuyar gaske. Ana dai zargin kungiyar da jerin hare hare a yankin Maiduguri.