Asusun UNICEF ya kai agajin farko a Somalia

Masu karbar taimakon UNICEF
Image caption Masu karbar taimakon UNICEF

Asusun kula da yara kanana na Majalisar Dinkin, UNICEF, ya kai kayan agaji na abinci da magunguna ga yara masu fama da yinwa a yankin Baidoa na Somalia.

Wannan shi ne karon farko da aka iya kai kayan agaji tun bayan da Kungiyar Al-Shabbab ta dage haramcin shiga yankin ga kungiyoyin agaji na kasashen waje.

Wata jami'ar UNICEF a Somalia ta ce,an bar su sun shiga ba tare da karbar harajin da Alshabab ta sanya ba.

Tun farko, Sakataren kula da raya kasashen waje na Birtaniya, Andrew Mitchel ya ce mata da yara kanana dake cikin Somalia za su ci gajiyar sababbin mataakan agajin gaggawa da kasarsa ke dauka.

Sakataren ya ce, Birtaniya na daukar matakan ne saboda abu ne mai muhummanci a ga cewa matsalar karancin abinci ba ta tilastawa 'yan Somalia ketara iyaka zuwa Kenya da Habasha, inda sansanonin masu gudun hijira suka cika suka batse ba.

Sai dai kuma Mr Mitchel wanda ya ke wata ziyarar a sansanin Dadaab ya ce, babu ruwansu da kungiyar Al-shabaaba wadda ke iko da wasu sassan kasar Somalia.

Andrew Mitchell ya bayyana cewar ya kadu da wasu daga labaran da ya ji daga yan gudun hijirar a Dadaab. Wata mata daga Somalia ta ce tana daga cikin wani gungun wasu mutanen 20 da suka dabi sayyada na tsawon fiye da kwanaki 30 daga wani kauye a tsallaken kan iyaka zuwa Kenya.

A wannan tafiya mawuyaciya, yan fashi sun tare su, suka kuma yi wa wasu daga cikin matan fyade.

Sakataren kula da raya kasashen wajen na Birtaniya ya ce ,wani sashe na gabacin Afrika da kuma kusurwar gabacin Afrikar na a kan wani siradi, kuma muddun kasashen duniya ba su hada kai domin tinkarar wannan matsala ba, to kuwa za ta iya zama wani bala'i.

Duka duka dai Birtaniya ta yi ta yi alkawarin bayar da kusan Fam miliyan casa'in tun farkon watan Yuli domin taimaka wa wadanda farin ya shafa.