Jana'iza ta rikide zuwa zanga zanga a Syria

Rohotanni daga Syria na nuni da cewa janaizar masu fafutuka 'yan adawa da aka kashe ranar juma'a run rikide zuwa wata zangar zangar kin jinin gwamnati.

Wasu hotunan bidiyo da aka wallafa a wasu shafukan internet sun nuno dubban 'yan adawa dauke da makara suna bi ta titunan birnin Damascus suna rera wakokin kin jin gwmanati.

A daya bangaren kuma, gidan telbijin mallakar gwamnatin kasar ya ce an kashe wasu dakarun gwamnati guda biyu.

Sai dai masu mafufutuka sun musanta zancen, suna cewa dakurun gwmanti ne suka bude wa farar hula wuta.